Gesponsert

Babbar Dama Ga Daliban Najeriya:  shirin tallafa wa kirkire kirkiren ɗalibai da ake kira Student Venture Capital Grant (S-VCG),

0
2KB

Babbar Dama Ga Daliban Najeriya: 

Ma’aikatar Ilimi ta Tarayya ta ƙaddamar da sabon shirin tallafa wa kirkire kirkiren ɗalibai da ake kira Student Venture Capital Grant (S-VCG), wanda ke bayar da tallafin Naira Miliyan 50 ba tare da ɗaukar kaso daga jarin kamfani ba.

Ministan Ilimi, Dr. Tunji Alausa, ne ya sanar da hakan a wani taron manema labarai a Abuja, inda ya ce shirin na daga cikin ginshiƙan Renewed Hope Agenda na gwamnatin Shugaba Bola Tinubu domin farfaɗo da harkokin kere kere a jami’o’i da kwalejojin ƙasar.

Shirin zai baiwa ɗalibai da ke da ƙirƙira a fannoni kamar Kimiyya, Fasaha, Injiniya, Lissafi da Harkokin Lafiya damar samun tallafin N50m domin haɓaka tunaninsu zuwa kasuwa.

Masu cin gajiyar shirin za su samu Horo na musamman da shigar da su cikin kasuwanci Jagoranci daga kwararru a fannin kasuwanci Kayan aiki da samar da dandalin ci gaban fasaha domin gina kamfanoni masu ɗorewa

Ma’aikatar Ilimi ta kuma sanar da haɗin guiwa da Google, wanda zai saka fasahar “evaluation agents” da Gemini AI cikin tsarin tantance aikace aikacen.

Duk wanda ya kammala shigar da aikace aikacensa cikin nasara zai samu lasisin Google Gemini Pro na shekara guda kyauta, tare da kayan koyon fasaha domin inganta basirar kasuwanci.

Ma’aikatar ta ce wannan haɗin gwiwar na da nufin “bada kayan aikin zamani ga ɗaliban Najeriya domin fara tafiyar da kasuwancinsu da sahihin kayan aiki.”

An buɗe shafin neman tallafin ga dukkan ɗaliban Najeriya da ke karatu a makarantu da gwamnati ta amince da su: Latsa Nan Domin Cikewa Yanzu

Suche
Kategorien
Mehr lesen
Andere
Probiotics in Poultry Market Size, Share, Trends, Key Drivers, Demand and Opportunity Analysis
"Future of Executive Summary Probiotics in Poultry Market: Size and Share Dynamics Data...
Von Kajal Khomane 2025-11-14 10:09:42 0 545
Andere
Global Drive-by-Wire Market Overview and Future Growth Trends
The automobile sector is still one of the most crucial sectors shaping industrial as well as...
Von Priya Sing 2025-11-11 15:31:46 0 523
Andere
Sand Control Systems Market Size driven by rising energy exploration and deepwater drilling investments
As per Market Research Futute, the Sand Control Systems Market Size is experiencing significant...
Von Suryakant Gadekar 2025-11-12 11:20:16 0 301
Andere
Vinegar Market Size, Share, Trends, Key Drivers, Demand and Opportunity Analysis
"Executive Summary Vinegar Market Opportunities by Size and Share The global vinegar...
Von Kajal Khomane 2025-10-23 11:14:54 0 1KB
Gesponsert