Gwamnatin Tarayyar ta sanar da fara horar da kusan matasa miliyan É—aya a Æ™arÆ™ashin shirin Technical and Vocational Education and Training (TVET) wani shiri mai sauya tunani daga Ma’aikatar Ilimi ta Tarayya da aka tsara domin samar da ‘yan kasuwa maimakon masu neman aiki.
Ministan Ilimi, Dr. Maruf Tunji Alausa (CON), ne ya bayyana haka yayin ziyarar sa ta duba cibiyoyin horarwa na AFS Vocational Hub, Garki, da Golden Finger Farms and Ranches Ltd, Abuja. Ya bayyana cewa matasa sama da 250,000 ne suka fara samun horo a cibiyoyi 2,600 a fadin kasar, wanda ya ce babban ci gaba ne a karkashin shirin “Renewed Hope” na Shugaba Bola Ahmed Tinubu.
Dr. Alausa ya ce Ma’aikatar ta takaita fannoni 86 zuwa sassa 28 masu muhimmanci kamar yadda suka hada da dinkin kaya, kiwon dabbobi, gyaran bututu, gyaran wayoyin GSM, da noma na zamani. Manhajar karatun ta kunshi kashi 90% na aiki a hannu da kuma kashi 10% na karatu a aji, domin tabbatar da kwarewa ta gaske.
An samu fiye da aikace aikace miliyan 1.3, inda aka tantance mutum 960,000 ta hanyar NIN da BVN. Kowane mahalarta zai rika karÉ“ar 22,500 a wata, yayin da cibiyar da take horar da su za ta karÉ“i 45,000 ga kowane É—alibi. Bayan kammala horo, za a ba su kayan farawa da damar samun rancen BOI mai karancin ruwa (single digit loan) domin kafa Æ™anana da matsakaitan sana’o’i.
Dr. Alausa ya kuma tabbatar da cewa kashi 5% na kasafin TETFund an ware shi musamman don TVET, domin tabbatar da dorewar shirin da faÉ—aÉ—a shi a fadin Æ™asa. A cewarsa, “Ilimin sana’o’i da fasaha yanzu yana tsakiyar ajandar cigaban Æ™asarmu.”
Boriowo Folasade
Daraktan Yada Labarai da Hulda da Jama’a,
Ma’aikatar Ilimi ta Tarayya