Web Analytics

ترقية الحساب

KARIN HASKE Shirin TVET INITIATIVE: Abubuwan Daya kamata ku sani

KARIN HASKE Shirin TVET INITIATIVE na ci gaba da tafiya yadda ake so. Jiya cikin dare dubban mutane sun samu saƙo ta imel, musamman waɗanda suka cike ɓangaren da ya shafi dinki kamar Fashion Design da Garment Making, wato masu haɗa kaya na sanyi.
Waɗanda suka yi apply a wannan ɓangaren an tura musu saƙo cewa akwai wani ɓangare na musamman da ya shafi Leather Workers.
Menene Leather Workers?
Leather Workers su ne masu sana’ar da ta shafi haɗa takalma da jakunkuna.
Shirin TVET Initiative ya buɗe dama ga waɗanda suka zabi ɓangaren Fashion Design dasu iya chanzawa zuwa ɓangaren Leather Workers gawadanda suka ga sako
Wannan saƙo ba daga scammers ba ne, daga hukumar TVET Initiative ne, kuma duk wanda yake buƙatar canji sai ya bi hanyar da aka turo masa a cikin Email ɗinsa.