LABARAN SAFIYAR LAHADI
12/10/1447AH - 05/10/2025CE
Ga takaitattun labaran safiyar nan.
Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kano ta kama wani mutum da ake zargi da hannu wajen sace Hakimin Garin Garun Babba, Alhaji Abdulmumini Mudi Zakari, wanda aka sace a shekarar 2023.
Tsohon Shugaban Ƙasa, Goodluck Jonathan, ya musanta jita-jitar da ake yadawa cewa ya danganta tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari da ƙungiyar Boko Haram.
Jami’ar Ibadan ta kaddamar da sabon sashen karatu ta intanet domin bai wa ɗalibai damar karatu daga gida.
Manyan jami’an sojin Najeriya goma sha shida sun shiga hannun hukumomi bayan zargin su da karya ƙa’idar aiki.
Jami’ar Nsukka ta bayyana cewa takardar shaidar digirin Ministan Fasaha, Uche Nnaji, ta bogi ce.
Gwamnan Jihar Jigawa ya kaddamar da shirin tallafawa mata dubu ɗaya da ɗari huɗu (1,400) da kayan ɗinkin hula, domin ƙarfafa harkokin sana’a da bunƙasa tattalin arziki.
Rundunar ’Yan Sanda ta kama mutum huɗu a Jihar Yobe da ake zargi da aikata manyan laifuka.
Yau take ranar Malamai ta Duniya.
Ruwan sama mai yawa ya lalata wasu gadoji da hanyoyi a jihohin Taraba, Kebbi da Filato.
A Jihar Kwara, rahotanni sun ce gundumomi tara suna cikin matsanancin hali, yayin da ‘yan bindiga ke tilasta mutane su basu abinci da abin sha a matsayin fansa.
Isra’ila da Hamas za su fara tattaunawa yau Lahadi, bayan matsin da Hamas ta fuskanta daga bangaren diflomasiyya da soja.
A Somalia, kungiyar Al-Shabab ta kai hari kan gidan yari a birnin Mogadishu.
Kungiyar Real Madrid na shirin sayen dan wasan Manchester City, Rodri, tare da shirin biyan fam miliyan 130.
Liverpool na kuma shirin kashe adadin kuɗi fam milyam 130 domin daukar dan wasan Bayern Munich, Michael Olise, a matsayin wanda zai maye gurbin Mohamed Salah.
Tsohon kocin Barcelona, Xavi, ya ce bai amince da tayin kungiyoyin Saudiyya ba, yana kuma a shirye idan aikin kocin Manchester United ya bude.
Bayern Munich ta bayyana golan AC Milan, Mike Maignan, a matsayin wanda zai maye gurbin Neuer, wanda yanzu ke da shekaru 39.
A sakamakon wasannin jiya:
Chelsea ta doke Liverpool da ci 2 da 1.
Real Madrid ta doke Villarreal 3 da 1.
Girona ta lallasa Valencia 2 da 1.
Inter ta doke Cremonese 4 da 1.
Bayern Munich ta samu nasara akan Frankfurt da ci 3 da 1.

·525 Vue
·1 Parts