Sponsor
Hukumar Civil Defence, Correctional, Fire and Immigration Services Board (CDCFIB) ta fitar da sunayen waɗanda suka cancanci shiga matakin jarabawar Computer Based Test (CBT) domin daukar ma’aikata na hukumomin tsaro.

Wannan na kunshe ne cikin wata sanarwa da Sakataren Hukumar, Manjo Janar mai ritaya Abdulmalik Jubril, ya fitar a ranar Laraba a Abuja.

Rahoton Kamfanin Dillancin Labarai na Ƙasa (NAN) ya bayyana cewa hukumomin da abin ya shafa sun haɗa da:

1. Hukumar Gyaran Hali ta Najeriya (NCoS)
2. Hukumar Shige da Fice ta Najeriya (NIS)
3. Hukumar Kashe Gobara ta Tarayya (FFS)
4. Hukumar Tsaro ta Civil Defence (NSCDC)

Hukumar ta bayyana cewa daga ranar Alhamis, 30 ga Oktoba, 2025, duk masu neman aikin za su iya ziyartar shafin hukumar na yanar gizo domin duba ko sun shiga jerin waɗanda aka zaɓa, da kuma wurin da za su gudanar da jarabawar CBT.

Sanarwar ta kuma shawarci masu neman aiki da su kula da sahihin adireshin shafin hukumar domin gujewa fadawa hannun masu damfara.
Hukumar Civil Defence, Correctional, Fire and Immigration Services Board (CDCFIB) ta fitar da sunayen waɗanda suka cancanci shiga matakin jarabawar Computer Based Test (CBT) domin daukar ma’aikata na hukumomin tsaro. Wannan na kunshe ne cikin wata sanarwa da Sakataren Hukumar, Manjo Janar mai ritaya Abdulmalik Jubril, ya fitar a ranar Laraba a Abuja. Rahoton Kamfanin Dillancin Labarai na Ƙasa (NAN) ya bayyana cewa hukumomin da abin ya shafa sun haɗa da: 1. Hukumar Gyaran Hali ta Najeriya (NCoS) 2. Hukumar Shige da Fice ta Najeriya (NIS) 3. Hukumar Kashe Gobara ta Tarayya (FFS) 4. Hukumar Tsaro ta Civil Defence (NSCDC) Hukumar ta bayyana cewa daga ranar Alhamis, 30 ga Oktoba, 2025, duk masu neman aikin za su iya ziyartar shafin hukumar na yanar gizo domin duba ko sun shiga jerin waɗanda aka zaɓa, da kuma wurin da za su gudanar da jarabawar CBT. Sanarwar ta kuma shawarci masu neman aiki da su kula da sahihin adireshin shafin hukumar domin gujewa fadawa hannun masu damfara.
0 Reacties 0 aandelen 42 Views
Sponsor