Gwamnatin Tarayya Ta Ƙaddamar Da Shirin “Next Moonshot” Da Zai Bada Damar Samun Tallafin Naira Miliyan 50 Ga Ɗalibai Masu Ƙirƙire-ƙirƙire
Ma’aikatar Ilimi ta Tarayya ta ƙaddamar da sabon shirin tallafa wa kirkire-kirkiren ɗalibai da ake kira Student Venture Capital Grant (S-VCG), wanda ke bayar da tallafin Naira Miliyan 50 ba tare da ɗaukar kaso daga jarin kamfani ba.
Ministan Ilimi, Dr. Tunji Alausa, ne ya sanar da hakan a wani taron manema labarai a Abuja, inda ya ce shirin na daga cikin ginshiƙan Renewed Hope Agenda na gwamnatin Shugaba Bola Tinubu domin farfaɗo da harkokin kere-kere a jami’o’i da kwalejojin ƙasar.
Shirin zai baiwa ɗalibai da ke da ƙirƙira a fannoni kamar Kimiyya, Fasaha, Injiniya, Lissafi da Harkokin Lafiya damar samun tallafin N50m domin haɓaka tunaninsu zuwa kasuwa.
Masu cin gajiyar shirin za su samu:
• Horo na musamman da shigar da su cikin kasuwanci.
• Jagoranci daga kwararru a fannin kasuwanci
• Kayan aiki da samar da dandalin ci gaban fasaha domin gina kamfanoni masu ɗorewa
Ma’aikatar Ilimi ta kuma sanar da haɗin guiwa da Google, wanda zai saka fasahar “evaluation agents” da Gemini AI cikin tsarin tantance aikace-aikacen.
Duk wanda ya kammala shigar da aikace-aikacensa cikin nasara zai samu lasisin Google Gemini Pro na shekara guda kyauta, tare da kayan koyon fasaha domin inganta basirar kasuwanci.
Ma’aikatar ta ce wannan haɗin gwiwar na da nufin “bada kayan aikin zamani ga ɗaliban Najeriya domin fara tafiyar da kasuwancinsu da sahihin kayan aiki.”
An buɗe shafin neman tallafin ga dukkan ɗaliban Najeriya da ke karatu a makarantu da gwamnati ta amince da su kamar haka: svcq.education.gov.ng
- Art
- Causes
- Crafts
- Dance
- Drinks
- Film
- Fitness
- Food
- Игры
- Gardening
- Health
- Главная
- Literature
- Music
- Networking
- Другое
- Party
- Religion
- Shopping
- Sports
- Theater
- Wellness