Labaran Safiyar Litinin, 13/10/1447AH - 06/10/2025CE.
Ga takaitattun labaran
Adadin mai da Najeriya ke hakowa ya ƙaru da kashi 762.5 cikin ɗari, bisa rahoton masana'antar mai ta ƙasa.
Jam’iyyar ADC ta zargi Shugaba Tinubu da rashin mai da hankali kan yadda matsalar tsaro ke ƙara taɓarɓarewa a ƙasar nan.
Ministan sufuri, Adegboyega Oyetola, ya ce Najeriya za ta ci gaba da nasarar shirin Deep Blue, tare da ƙoƙarin mayar da ƙasar kujerarta a hukumar IMO ta duniya.
Rundunar sojin Najeriya ta tsare jami’anta guda 16 bisa zargin saba ƙa’idar aiki.
Gwamnatin Tarayya ta bayyana farin ciki kan asibitin tiyatar hanta mai zaman kansa da aka gina a Najeriya da kuɗi Naira biliyan takwas (N8b).
Dakarun sojin Najeriya sun lalata matatun hakar ma’adinai na haram a wasu sassan ƙasar.
Rikicin cikin gida na jam’iyyar PDP a Jihar Edo ya ƙara kamari, bayan bangaren Wike ya zabi sabbin shugabanni.
Al’ummar ƙaramar hukumar Kebbe a Jihar Sokoto sun roƙi gwamnati ta ba su damar mallakar makamai domin kare kansu daga harin ƴan bindiga.
Hukumar FRSC ta tabbatar da mutuwar mutane huɗu a hatsarin mota da ya auku a tititin Kaduna-Abuja.
Kotun tarayya a Abuja ta ƙi amincewa da buƙatar Ministan kimiyya, Uche Nnaji, wanda yake neman hana Jami’ar Nsukka (UNN) fitar da bayanan karatunsa.
Gwamna Uba Sani na Kaduna ya amince da biyan Naira biliyan 2.3 ga tsofaffin ma’aikata da iyalan waɗanda suka rasu.
A Jihar Ondo, ƴan sanda sun kama wani mutum bisa zargin yi wa yarinya ’yar shekara shida duka a garin Ore.
Rundunar ƴan sanda a Jihar Lagos ta kai samame a wani otel da masu laifi ke amfani da shi, inda ta kama mutane biyu.
Kotun jihar Oyo ta soke dakatar da ƙungiyar NURTW da Gwamna Seyi Makinde ya yi.
Ƴan fashin daji sun kashe ɗaya daga cikin kwamandojin maharba a yankin Gangara, ƙaramar hukumar Giwa, Jihar Kaduna.
A ƙasashen waje, hukumomin China sun ce ma’aikatan ceto a Tibet na ƙoƙarin kaiwa mutane kusan 1,000 da suka makale a tsaunin Everest, mafi tsawo a duniya.
Babban hafsan sojin Isra’ila ya ce idan tattaunawa da ƙungiyar Hamas ta gaza, za su koma yaƙi a Zirin Gaza.
Firaministan Georgia na neman soke manyan jam’iyyun adawa a ƙasarsa.
A Nepal, mutane 47 sun mutu sakamakon zabtarewar ƙasa da ambaliyar ruwa.
A Faransa, Firaminista Lecornu ya kafa sabuwar majalisar ministoci.
A Jamhuriyar Dimokuraɗiyyar Congo, ƴan tawayen CODECO sun kashe mutane 14 a lardin Ituri da ke arewacin ƙasar.
A gasar Premier League, Manchester City ta doke Brentford da ci 1-0.
A La Liga, Celta Vigo da Atletico Madrid sun tashi 1-1.
A Serie A, Napoli ta doke Genoa da ci 2-1, yayin da Juventus da AC Milan suka tashi 0-0.

·821 Просмотры